<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>20</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka.
 Kai ka kawo dukanmu yinin nan da lafiya
 Muna rera waƙarmu, muna maka godiya.

[V2]
 2) In yau wata jaraba za ta kai mu haɗari,
 Ba mu ikon jurewa, ƙara mana ƙarfi kuwa,
 Kiyaye mu lafiya, har mu ka da zunubi.

[V3]
 3) Bisa ga maganarka, daidaita rayukanmu,
 Bishe mu da Ruhunka, amshi mulkin nufinmu.
 Bar mu miƙa gare ka hadaya ta zuciyarmu.

[V4]
 4) Ji yanzu addu'armu, ji mu, muna roƙonka.
 Da mu duk da ƴanuwa, baiwarka mafificiya
 Ita ce bukatarmu, sahihiyar zuciya.

[V5]
 5) Haka za mu bayyana yau da gobe godiyarmu.
 Haka za mu ɗaukaka sunan Ubangijinmu.
 Za mu shaida yabonka, Almasihu Allahnmu.</lyrics>
<title>Yesu Ubangijinmu, Ga Mu Nan A Gabanka LW20</title>
</song>